"Afuwa ga 'yan kungiyar Boko Haram"

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Boko Haram ta dade tana kai hare-hare a sassa da dama na Najeriya

Shugabannin majalisar dokokin Najeriya sun nemi da a yiwa 'ya'yan kungiyar Boko Haram afuwa bisa hare-haren da suke kaiwa a kasar a matsayin wata hanya ta yin rigakafin aukuwar irin haka a nan gaba.

Shugaban Majalisar wakilai ta kasar Aminu Tambuwal ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar a yiwa 'ya'yan kungiyar afuwa bisa abubuwan da suka aikata, domin samun zaman lafiya mai dorewa.

Shi ma a nasa bangaren shugaban majalisar dattawa na kasar Sanata David Mark, ya yi kiran da a yafewa wadanda suka kai hare-haren na Kano, a matsayin wata hanya ta yin rigakafin aukuwar irin haka a nan gaba.

Duka jami'an suna magana ne bayan sun kai ziyara birnin Kano inda hare-haren da kungiyar ta kai suka yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla da 150.

Sai dai kalaman na su na zuwa ne bayan da shugaban kasar Goodluck Jonathan ya ce a shirye hukumomin tsaro suke "su murkushe masu kai hare-haren ta'addanci a kasar".

Addu'ar zaman lafiya

An nemi al'umar Musulmi da Kirista a jihar ta Kano da su gudanar da addu'o'i domin samun zman lafiya.

Tuni aka gudanar da addu'o'i na musamman a kusa da fadar mai Martaba Sarkin Kano, domin bukatar Allah ya taimaka wajen kawo karshen tashe-tashen hankula.

Jami'an 'yan sanda sun ce an gano bama-bamai 12 kirar gida a wata mota da aka ajiye a birnin.

Likitoci sun ce ana ci gaba da kawo gawarwaki zuwa mutuware kuma adadin wadanda suka mutu sakamakon harin za su iya karuwa.

'A kawo karshen tashin hankali'

Wakilin BBC a Kano ya ce wasu mutane sun fara komawa ayyukansu na yau da kullum, amma akwai dinbin jami'an tsaro a kan tituna. Akwai kuma dokar hana yawon dare.

Gwamnatin Kano da fadar Sarki ne suka kira da a gudanar da addu'o'i a gidajen rediyon jihar.

An umarci duka Musulmi da Kirista su gudanar da addu'o'i a wuraren ibadarsu.

Wakilinmu ya ce akalla mutane 200 ne suka halarci addu'a a babban masallacin birnin, yayin da aka gudanar da addu'o'in a sauran masallatai na birnin.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan ne hari mafi muni da kungiyar ta kai kawo yanzu

Birnin Kano ne gari mafi girma a arewacin Najeriya inda Musulmai suke da gagarumin rinjaye, amma akwai mabiya addinin Kirista 'yan kadan.

'Alwashin murkushe 'yan ta'adda'

Boko Haram ta sha kai hare-hare kan mabiya addinin Kirista da kuma Musulmai, ta kuma nemi 'yan kudancin kasar da su bar yankin Arewacin kasar.

Daruruwan mutane ne suka bar gidajensu sai dai rahotanni sun ce wasu jama'ar na taimakawa 'yan uwansu.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kai ziyara Kano ranar Lahadi domin ta'aziyya, sannan ya sha alwashin murkushe "yan ta'adda".

Sai dai wakilinmu ya ce har yanzu jama'a na dari-dari, saboda sun sha jin irin wannan alkawarin a baya.

Wannan shi ne hari mafi muni da kungiyar ta kai, sai dai ta kashe daruruwan mutane a 'yan kwanakin nan.

Wani likita ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa adadin wadanda suka mutu a harin na ranar Juma'a zai iya kaiwa 250.

Karin bayani