Kotun ICC za ta zauna kan jami'an gwamnatin Kenya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Luis Moreno Ocampo

A ranar Litinin ne alkalan kotun hukunta masu aikata manyan laifuka da ke Hague za su ba da sanarwa akan ko wasu fitattun 'yan siyasar kasar Kenya guda shida za su fuskanci shari'a game da tashe- tahen hankulan da suka biyo bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a shekarar 2007.

An yi taho-mu-gama tsakanain magoya shugaba Miu Kibaki da na abokin hamayarsa, Raila Odinga ne a lokacin da ake sanar da sakamakon zaben.

Fiye da mutane dubu ne suka mutu sannan wasu kusan rabin miliyan suka yi gudun hijira sakamakon hargitsin da ya biyo bayan zaben.

An kai batun gaban kotun ICC ne, bayan kotun ta aike da babban mai shigar da kararta, Luis Moreno Ocampo, zuwa kasar don gudanar da bincike game da abin da ya yi sanadiyar rikicin bayan zaben.

Luis Moreno Ocampo ya yi amannar cewa ba haka kwatsam rikice-rikicen bayan zaben kasar suka faru ba, illa dai wasu fitattatun 'yan siyasa ne suka kitsa su.

Fitacce daga cikin wadanda ake tuhuma shi ne Uhuru Kenyatta - wanda a halin yanzu shi ne mataimakin Firayim Minista, kuma dan shugaban kasar na farko ne.