Tattalin arzikin duniya na cikin matsala

Tattalin arzikin duniya na cikin matsala Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kasashe da dama a duniya na cikin matsala

Hukumar Bayar da Lamuni ta Duniya IMF, ta yi sauyi sosai a kan hasashenta dangane da ci gaban tattalin arziki a duniya sakamakon matsalolin tattalin arzikin da ake fuskanta.

Hukumar ta rage hasashenta da kamar sulusin kashi guda a cikin dari.

Matsalar tattalin arzikin da kasashen Turai ke fama da ita ce ta jawo rauni ga hasashen ci gaban tattalin arzikin.

Masana tattalin arzikin Asusun an IMF sun bayyana cewa irin habakar da tattalin arzikin duniya ke yi ta ragu , yayin da hadarin da tatalin arzikin kan fuskanta ya karu sosai a shekarar da ta gabata.

Yanzu kuma masanan sun fara hasashen cewa za a fuskanci durkushewar tattalin arziki a tsakanin kasashe masu amfani da kudin Euro, musamman ma kasashen Italiya da Spain.

An dai gina wannan hasashen ne a kan kokarin da ake yi na tunkarar matsalalar tattalin arzikin da kasashe masu amfani da kudin Euro ke fuskanta.

Za a iya shawo kan matsalar

Asusun ba da Lamuni na duniyar ya yi gargadin cewa hadarin tabarbarewar tattalin arzikin da kasashen Turai ke fuskanta na ci gaba da karuwa, kuma yana iya janyo koma-baya ga habakar tattalin arziki.

Rahoton dai ya bukaci Gwamnatoci da su tsaya tsayin-daka wajen daukar kwararan matakai don shawo kan lamarin.

Ya kara da cewa yanzu galibin kasashe masu wadata na bakin kokarinsu wajen kara nauyin aljufan gwamnatocinsu.

Kodayake rahoton ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen Amurka da Japan su fito da kawararan shirye-shirye.

A cewar babban jami'in tattalin arziki na IMF, Olivier Blanchard ya ce lamarin bai yi munin da zai ki jin magani ba.

"Idan aka dauki matakan da suka dace, alal hakika za a iya kauce wa matsalar, haka kuma tattalin arzikin zai iya komawa kan turbar habaka da bunkasa.

Za a iya daukar wadannan matakan, kuma akwai bukatar daukarsu, kazalika akwai bukatar daukarsu cikin gaggawa".

Haka kuma Asusun ya bukaci wasu kasashe da su sake tunani game da irin hanzarin da suke yi wajen rage cin bashi.

Duk da cewa rahoton bai ayyana sunayen kasashen ba, ana ganin cewa idan dai biri ya yi kama da mutum, to Asusun bayar da Lamunin na kokarin yin shagube ne cewar gwamnatin kasar Jamus ta dage wajen rage bashin da take ci cikin gaggawa.

Karin bayani