Obama ya yaba kan sanyawa Iran tukunkumi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barack Obama

Shugaba Obama na Amurka ya yi maraba da takunkumin da Tarayyar Turai ta sanyawa Iran inda ya ce hakan ya nuna cewa a shirye duniya take ta dakatar da Tehran daga shirinta na kera makaman nukiliya.

Takunkumin da aka amince a sanyawa Iran a ranar Litinin dai ya hada da haramta shigo da danyen mai daga kasar da kuma kwace kadarorin da babban bankin Iran ya mallaka a wasu kasashe.

Gwamnatin Amurka ta kuma bayar da sanarwar sanya takunkumi akan Bankin Tejarat, wanda shi ne banki na uku mafi girma a kasar ta Iran.

A martanin da ta mayar, Iran ta sake nanata barazanar da ta yi ta toshe mashigar nan ta Hormuz.

Farashin mai ya tashi zuwa kusan dala dari kan kowacce ganga a birnin New York na Amurka bayan an samu wannan labari.