An haramta zanga-zanga a titunan Senegal

Abdoulaye Wade
Image caption Shugaba Abdoulaye Wade na Senegal

Gwamnatin kasar Senegal ta bayar da sanarwar haramta duk wata zanga-zanga a kan tituna tun daga gobe Alhamis, yayin da Majalisar Tsarin Mulkin kasar ke yanke shawara a kan yiwuwar baiwa Shugaban kasar, Abdoulaye Wade, damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na uku.

An sake zaben Shugaban kasar ne, dan shekaru tamanin da biyar a duniya, a shekarar 2007 a karkashin sabon kundin tsarin mulkin kasar bayan da aka takaita wa’adin shugabanci zuwa shekaru biyar kadai.

Tuni dai yunkurinsa na sake tsayawa takarar shugabancin kasar ya haddasa tashe-tashen hankula.

Ranar Juma’a ne Majalisar Tsarin Mulkin za ta yanke shawara.

Mataimakin Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka mai kula da nahiyar Afirka, William Fitzgerald, ya ce yunkurin Mista Wade na sake tsayawa takarar abin takaici ne.