Shugabannin Afirka sun hallara a Habasha

Jean Ping Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban hukumar Tarayyar Afirka, Jean Ping

Shugabannin kasashen Afirka sun hadu a Habasha don halartar babban taron shekara-shekara na kungiyar Tarayyar Afirka, AU, a wannan makon.

Babban batun da za a tattauna a kansa dai shi ne zaben sababbin jami'an da za su kula da ayyukan hukumar Tarayyar.

Afirka ta Kudu ta kara kaimi don ganin 'yar takararta ta jagoranci hukumar.

Hankoron samun goyon baya don darewa mukami mafi girma a hukumar Tarayyar dai zai kara tsananta da safen nan lokacin da Majalisar Zartarwar Tarayyar za ta zauna don yin nazari a kan 'yan takarar da ke gaba-gaba.

Za a yi nazari a kan ayyukan da shugaban hukumar mai ci, Jean Ping, ya gudanar a baya, yayin da yake kokarin gamsar da kasashen da ke Tarayyar su sake zabensa.

Sai dai kwararren jami'in diflomasiyyar kuma masanin tattalin arziki yana fuskantar kalubale daga ministar harkokin cikin gida ta Afirka ta Kudu, Dokta Nkosozana Dlamini Zuma.

Ya zuwa yanzu dai takarar mukamin shugaban ce ta fi zafi duk da cewa mutane biyu ne kacal ke hararar kujerar. Ba wanda ya kalubalanci mataimakin shugaban hukumar mai ci, Erastus Mwencha.

Hakazalika, shugabannin kasashen na Afirka za su zabi sababbin kwamishinonin hukumar guda goma, wadanda a yau din ake nazari a kan takardunsu na neman aikin.

Sai dai kuma ana nuna matukar damuwa a kan kimar mutanen da ke fafutukar ganin sun jagoranci Tarayyar ta Afirka, wadda ke son sauya taku.

Michael Orwa, wakili a gamayyar kungiyoyin da ke sa-ido a kan rawar da kasashen Tarayyar ke takawa, ya bayyana cewa:

“Za mu so mu ga irin rawar da daidaikun kasashe ke takawa wajen amincewa da kuma aiwatar da yarjejeniyoyi ta yi tasiri wajen zabar mutanen da za su shugabanci Tarayyar Afirka. Alal misali, a ce kasar da ta amince ta kuma aiwatar da yarjejeniyoyi uku kacal ta shugabanci Tarayyar—wannan bai dace ba”.

Shugabannin na kasashen Afirka za su kuma duba yiwuwar habaka cinikayya a tsakaninsu, ganin yadda nazarce-nazarcen tattalin arziki na baya-bayan nan suka nuna cewa nahiyar na bunkasa.

Daga cikin batutuwan da za a duba yayin muhawarar akwai cire duk wasu dokoki da ke tarnaki ga harkar cinikayya a tsakanin kasashen.

Sai dai kuma yayin da shugabannin kasashen ke tattauna wadannan sauye-sauye, za a yi musu hannunka mai sanda cewa kananan 'yan kasuwa a nahiyar sun taimaka wajen bunkasar tattalin arziki da kuma samar da ayyukan yi.

Somaliya na cikin muhimman batutuwan da za a tattauna a taron na bana: za a duba hare-haren da dakarun Kenya da na Habasha suka kaddamar a 'yan kwanakin nan a kan mayakan sa-kai na kungiyar Al-Shabaab, da kuma shawarar da Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya yanke ta karo dakarun kiyaye zaman lafiya dubu goma, da ma yadda gwamnatin kasar mai shigowa za ta kasance bayan wa'adin gwamnatin rikon kwaryar da ke mulki ya kare a karshen watan Agusta.

Manazarta dai sun zuba ido su gani ko za a tsawatarwa Shugaba Omar al-Bashir na Sudan saboda yadda yake mua'mala da Sudan ta Kudu da kuma rikicin da ake tafkawa a jihar Kordofan.

Batutuwan da suka shafi kudi ma dai za su dauki hankali a wajen taron, a karo na biyu tun bayan mutuwar Shugaba Mu'ammar Gaddafi, daya daga cikin masu samawa Tarayyar kudade.

Image caption Sabuwar hwdkwatar Tarayyar Afirka a Addis Ababa

Shugabannin za su tafka muhawara a kan hanyoyin da za a bi don samar da dala miliyan dari biyu da saba'in din da Tarayyar ta kasafta don gudanar da ayyukanta bana.

Sannan kuma shugabannin za su tattauna batutuwan da suka shafi Afirka ne a sabon ginin hedkwatar Tarayyar na zamani, wanda China ta yi musu tukwici da shi.