An fitar da sakamakon zaben majalisa a Congo

Joseph Kabila Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Joseph Kabila na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo

Hukumar zabe ta Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo ta fitar da kusan daukacin sakamakon zabukan majalisar dokokin da aka gudanar ranar 28 ga watan Nuwamba.

Bayan ta kwashe watanni biyu tana ta raskwana da kokarin kare kanta daga zarge-zargen aikata magudi, hukumar zaben ta fitar da sunayen dari hudu da talatin da biyu a cikin mutane dari biyar din da za su shiga majalisar dokokin.

Har yanzu dai jam'iyyar Shugaba Joseph Kabila, PPRD, ce ta fi karfi a majalisar bayan da ta lashe kujeru hamsin da takwas, amma kuma kusan rabin kujerun da ta samu a zaben baya sun kubuce mata a wannan karon.

Jam'iyyun adawa dai ba su ko kusa kamo kafar jam'iyyar ta PPRD ba, amma kuma sai bangarorin biyu sun yi kawance da kananan jam’iyyu kafin su yi rinjaye a majalisar.

Sanarwar sakamakon dai ba za ta kawo karshen tashin-tashinar zabe a kasar ba—ana sa ran 'yan takara da dama za su nufi kotu don kalubalantar sakamakon.

Tuni dai hukumar zaben ta bukaci Kotun Kolin kasar ta bayar da umurnin a sake zabe, ta kuma hukunta 'yantakara, a mazabu bakwai inda aka samu tashe-tashen hankula.

Karin bayani