Jonathan ya kalubalanci Boko Haram da su fito a tattauna

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Boko Haram ce babbar matsalar da Goodluck Jonathan ke fuskanta tun bayan hawansa mulki

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kalubalanci kungiyar nan ta Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram da su fito su bayyana kansu su kuma bayyana bukatunsu a matsayin matakin farko na fara tattaunawa da su.

Shugaban ya kuma amince cewa amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen tashe-tashen hankulan ba.

Sai dai Jonathan ya kara da cewa, sabanin tsagerun Naija Delta, matsalar 'yan Boko Haram ita ce ba a san shugabanninta ba balle a tattauna da su.

Sai dai shugaban Kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya ce ba za su tattauna da gwamnatin Najeriyar ba.

A wata hira da kamfanin dillancin labarai na Reuters, Jonathan ya ce babu tantama kungiyar boko Haram tana da alaka da sauran kungiyoyi masu jihadi a ketaren Najeriya.

Akalla mutane 186 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da kungiyar ta kai a Kano ranar Juma'ar da ta gabata.

"Idan suka bayyana kansu, suka kuma ce ga dalilin da ya sa muke gwagwarmaya, ga dalilin da ya sa muke fito na fito da gwamnati, ga dalilin da ya sa muke lalata dukiyoyin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, to daga nan za a samu ginshiki na fara tattauna wa, in ji shugaba Jonathan.

Shugaban na Najeriya ya kuma kara da cewa, "Za mu tattauna da ku, ku sanar da mu matsalolinku, za mu warware muku su, amma idan ba su bayyana kansu ba, da wa za ka tattauna?"

Sai dai shugaban na Najeriya ya bayyana cewa akwai bukatar a kawo ayyukan ci gaba a yankunan arewacin kasar inda ake da dimbin matasa marasa aikin yi, abinda yake baiwa kungiyoyi masu tada kayar baya damar samun magoya baya cikin sauki.

"Amfani da karfin soji kadai ba zai kawo karshen hare-haren ta'addancin ba," in ji shi, "ana kuma bukatar a samar da yanayin da zai baiwa matasa damar samun ayyukan yi".

Mu muka kai hari Kano sai dai ...

Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Kungiyar Boko Haram ta ce ba za ta tattauna da jami'an Najeriya ba

Kungiyar ta Jama'atu Ahlus Sunna Lid-Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram ta sake fitar da wani sako na murya mai kunshe da muryar Shugaban Kungiyar, Abubakar Shekau a dandalin sakonnin bidiyo na You tube, inda suka sake jadda ikirarinsu na cewa su suka kai hari a Kano.

Shugaban Kungiyar, wanda ke sanye da farar riga da rigar sulke dauke da bindiga, ya yi jawabi na kusan minti arba'in a wannan bidiyo, inda yake bayyana cewa kungiyar ce ta kai hari ranar Juma'a a Kano, al'amarin da ya haddasa mutuwar mutane akalla 186.

Shugaban Kungiyar ya kuma kara yin gargadi ga mahukuntan Nigeriya da su guji kai masu hare hare da kokarin kama masu magoya baya.

Ya zargi jami'an tsaron Nijeriya da bindige fararen hula, bayan 'yan kungiyarsu sun kammala kai hare-hare a birnin na Kano.

Sai dai tuni jami'an tsaron najeriyar sun musanta wannan zargin.

Karin bayani