Kungiyar agajin likitoci ta MSF ta janye daga wasu sassan Libya

wasu yara a garin Misrata, Libya Hakkin mallakar hoto Reuters

Kungiyar nan mai bayar da agaji ta fuskar kiwon lafiya ta Medicins Sans Frontieres, ta dakatar da aikace-aikacenta a cibiyoyin da ake tsare da mutane a birnin Misrata na kasar Libya, saboda abun da ta kira azabar da aka ci gaba da ganawa mutane.

Darakta-Janar na kungiyar, Christopher Stokes, ya shaida wa BBC cewar babu wata tantama, azabar da ake ganawa mutane ce ke haifar da raunukan da suke samu.

Yace muna da likitoci na kungiyarmu da sauran ma'aikatan kiwon lafiya, wadanda suka hada da na kasashen waje, da ke aiki a Misrata, kuma raunukan da muke gani ba raunuka ba ne da aka samu a filin daga.

Wannan al'amari ya zo ne kwana kacal bayan da kwamitin sulhu na MDD ya yi gargadin cewar matsalar cin zarafin mutane na karuwa a wuraren da ake tsare mutane a kasar ta Libya.

Karin bayani