Mutane sama da dari ne suka mutu bayan shan gurbataccen magani a Pakistan

wasu daga cikin marasa lafiya a Pakistan Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption wasu daga cikin marasa lafiya a Pakistan

Mutane fiye da dari ne kawo yanzu aka san sun mutu a birnin Lahore na kasar Pakistan, a sakamakon shan wani gurbataccen maganin ciwon zuciya.

Likitoci sun ce akwai wasu mutanen kamar dari biyu da hamsin kwance a asibiti, inda ake yi musu magani.

An danganta mace-macen, wadanda suka faru a cikin makwanni ukkun da suka wuce, da wasu magungunan da ba su da inganci, wadanda ake bayarwa kyauta ga mutanen da suke fama da ciwon zuciya a wani asibitin gwamnati.

Jami'ai sun ce ana can ana gudanar da bincike.

Tuni aka kama wasu mutane uku da suka mallaki kamfanonin hada magunguna domin yin musu tambayoyi.

Daya daga cikin wadanda suka rasa dangi, ya ce mahaifinsa ya rasu ranar 23 ga watan Disamba bayan da ya sha wannan gurbataccen magani, inda yayi ta zubar da jini daga bakinsa da kuma mafitsara.