Shekau ya amsa cewa su suka kai hare-hare a Kano

 Malam Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Malam Abubakar Shekau

Kungiyar nan ta Ahlus Sunna Lid-Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram ta sake fitar da wani sako na murya mai kunshe da muryar Shugaban Kungiyar, Imam Abubakar Shekau a dandalin sakonnin bidiyo na You-tube.

Shugaban Kungiyar, wanda ke sanye da farar riga da rigar sulke dauke da bindiga, ya yi jawabi na kusan minti arba'in a wannan bidiyo, inda yake bayyana cewa kungiyar ce ta kai hari ranar Juma'a a Kano, al'amarin da ya haddasa mutuwar mutane akalla dari da tamanin da biyar.

Shugaban Kungiyar ya kuma kara yin gargadi ga mahukuntan Nigeriya da su guji kai masu hare hare da kokarin kama masu magoya baya.

Ya zargi jami'an tsaron Nijeriya da bindige fararen hula, bayan 'yan kungiyarsu sun kammala kai hare hare a birnin na Kano.

Malam Shekau ya kuma kawara da yuwuwar shiga wata tattaunawar sulhu da hukumomin Nijeriyar.

Karin bayani