An gabatar da sabon kuduri a kan Syria

Shugaba Bashar al-Assad Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Bashar al-Assad na Syria

Kasashen Turai da na Larabawa sun gabatar da daftarin wani kuduri wanda ke kira ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya goyi bayan wani shirin Kungiyar Kasashen Larabawa a kan rikicin Syria.

Kudurin dai na neman goyon bayan Kwamitin Sulhun ne ga shirin Kungiyar Kasashen Larabawa a kan Syria.

Abu mafi muhimmanci a cikin kudurin shi ne cewa ya amince da kiran da kasashen Larabawan suka yi ga Shugaba Bashar al-Assad ya mika mulki ga mataimakinsa, wanda shi kuma zai samar da wani shiri na sauyin shugabanci da hadin gwiwar wata gwamnatin hadin kan kasa.

Sai dai jami'an diflomasiyya sun ce za a ci karo da matsaloli: Rasha ta nace cewa ba za ta goyi bayan duk wani mataki wanda zai kawo sauyin gwamnati ba.

Akwai kuma damuwa cewa gargadin daukar karin matakai idan Syria ba ta bayar da kai bori ya hau ba ka iya kaiwa ga tsoma bakin kasashen waje.

Sai dai kuma Rasha ta ce a shirye take ta tattauna a kan kalaman kudurin.

Hakan na nufi ke nan akwai yiwuwar kasar ta Rasha, wadda ita ce babbar kawar Syria a Kwamitin Sulhun, ta sassauta matsayinta.

Kasashen Yamma dai na fatan kiran na kasashen Larabawa zai tausasa zuciyar Rasha dangane da duk wani mataki da Kwamitin Sulhun zai dauka a kan Syria.

Don haka ne ma suka yi amfani da kalaman Kungiyar Kasashen Larabawan, yayin da jakadan Faransa ya ke cewa duk mai tambaya sai ya mika ta ga jami'an Kungiyar wadanda za su yi jawabi ga Kwamitin Sulhun ranar Talata.