CAN na adawa da nadin Sufeton 'yan sandan Najeriya

Mohammed Abubakar Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Mohammed Abubakar

Kungiyar Kiristoci ta Najeriya wato CAN, ta nuna rashin jin dadinta akan nada Mohammed Abubakar a matsayin sabon Sufeto Janar na 'yan sandan kasar, na wucin gadi.

A cewar kungiyar, bai kamata a ba shi wannan mukamin ba, saboda a cewar ta, yana daga cikin wadanda hukumar bincike akan rikicin Jos na shekara ta 2001, a karkashin jagorancin mai shari'a Niki Tobi, ta gano ya aikata ba daidai ba.

A cikin hirar da yayi da BBC, Pastor Ayo Orisejafor, shugaban CAN din, ya ce bai kamata irin wannan mutum ya rike mukamin Sufeto Janar na 'yan sandan ba.

A tsakiyar wannan makon ne gwamnatin Najeriya ta sanar da nadin Mohammed Abubakar, yayin da ta ce Sufeto Janar Hafiz Ringim ya tafi hutun karshe kamin ya wuce ritaya.

Karin bayani