Tattaunawa tsakanin kasashen Sudan a kan mai

Matatar mai a Sudan ta Kudu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Matatar mai a Sudan ta Kudu

Shugaban Jumhuriyar Sudan da takwaransa na kasar Sudan ta kudu na tattaunawa da juna, da nufin warware sabanin da ke tsakanin kasashen biyu game da harkar mai.

Ana fargabar sabanin zai haddasa sabon rikici a tsakanin kasashen biyu.

Shugabannin kasashen Ethiopia da Kenya, su ma za su kasance a wajen tattaunawar wadda za a yi a Addis Ababa.

Sudan ta Kudu, wadda ta samu 'yancin zama cikakkiyar kasa a watan Yulin bara, ta na fitar da mai zuwa kasashen waje ta bututan Jumhuriyar Sudan.

Sai dai kasashen biyu sun kasa jituwa a kan kudin da Sudan ta kudun za ta dinga biya, na amfanin da bututan man Jumhuriyar Sudan din.