Kungiyar Kasashen Larabawa ta dakatar da aikin masu sa-ido a Syria.

Zanga-zanga a Syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yara ma ba za a ba su labari ba

Kungiyar kasashen Larabawa ta dakatar da aikin tawagar masu sa-idonta da ke Syria.

Shugaban kungiyar, Nabil el Arabi, ya ce an yanke shawarar ne sabili da yadda yanayin ke kara tabarbarewa da kuma fadan da ake ci gaba da yi a Syria.

Sakataren kungiyar Ahmad Bin Hilly ya ce dakatar da masu sa idan zai ci gaba har sai ministocin hulda da kasashen waje na kungiyar sun yanke shawara kan aikin tawagar a nan gaba.

A yanzu masu sa idan za su ci gaba da kasancewa a Syrian.

Wannan matakin ya zo 'yan kwanaki kadan bayan an kara wa'adin tawagar zuwa wata na biyu.

Gwamnatin Syria dai ba ta ji dadin wannan shawarar ba, inda ta kwatanta ta a matsayin bambarakwai.

Mr El-Arabi na ta tattaunawa da Rasha, yana kokarin shawo kanta, ta goyi bayan wani kudurin kungiyar a kan Syria wanda ta kai Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya.

Yau kamar kwanaki goma ke nan tun da aka fahimci cewa fada kara kamari yake yi a Syria.

Dakarun gwamnatin Assad sun tashi tsaye a kan wadanda suka bayyana da 'yan ta'adda.

'Yan tawayen kungiyar Dakarun 'yantattar Syria sun kuma suna ta zafafa ayyukansu, suna cewa suna kare jama'a ne da gwamnati za ta iya halakawa.

Ana kuwa ganin su kiri-kiri a kan tituna a wasu unguwannin mabiya suna a gefen birnin Dimashqa.

Shawarar da Kungiyar Kasashen Larabawa ta yanke ta dakatar da ayyukan masu sa-ido dinta, ta fi alaka da siyasa maimakon tsaron lafiyar masu sa-idon.

Jagoran Kungiyar ta Larabawa ya ce sun yanke shawara ne bayan da gwamnatin Syria ta tsanaanta rikicin.

Wannan dai wata hanya ce ta karin matsin lamba a kan Syriar, a yayin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ke kan kada kuri'a a kan rikicin Syriar.

Biritaniya, da Faransa da Amurka suna goyon bayan shirin kungiyar Larabawan da ke kira ga Shugaba Assad ya yi murabus.

Russia dai tana ci gaba da kin goyon bayan duk wani abin da zai kai hambarar da gwamnati ko kuma tsoma baki daga waje.

Karin bayani