Kungiyar Boko Haram ta yi wa jihar Sakkwato barazana

Harin Boko Haram a Kano
Image caption Hankali yana tashe a Sakkwato

A Najeriya, kungiyar Jama'atu Ahlis Sunnati Lid Da'awati wal Jihad, wadda aka fi sani da Boko Haram, ta bukaci mahukunta a jihar Sakkwato da su gaggauta sakin wasu daga cikin mambobinta da suke zargin jami'an tsaro sun kame a jihar.

A wata hira ta wayar tarho da manema labarai, kakakin kungiyar ya yi gargadin cewa matukar ba a saki 'ya'yan kungiyar da jami'an tsaron suka kame ba, to kuwa za ta kaddamar da hare-hare a jihar Sakkwaton.

A waje daya kuma, rahotanni daga Kano a arewacin Nigeria na cewa an yi harbe-harbe dazu da magariba a ofishin 'yan sanda da ke Na'ibawa 'Yan katako.

Mazauna unguwar sun ce an shafe kimanin mintuna talatin suna jin amon bindigogi iri daban-daban a yankin, abin da ya tilasta musu shigewa gidajensu.

Wasu rahotanni na cewa an samu asarar rayuka a musayar wutar.

A nata bangaren rundunar 'yan sandan jihar Kano ta tabbatar da kai harin, inda ta ce jamia'nta sun maida martani.

Sai dai ba ta yi karin bayani kan jikkata ko asarar rayuka ba, domin ta ce har yanzu tana tattara bayanai.

Rahotannin dai na cewa zuwa yanzu komai ya lafa a yankin.

Akalla ofishishin 'yan sanda uku aka kai wa hari a birnin na Kano, tun bayan tashin bomabomai a wasu gine-ginen jami'an tsaro kimanin takwas a birnin kwanaki tara da suka wuce.

A jihar Enugu ta Najeriya kuma, rundunar 'yan sandan jihar ta musanta jita-jitar da ake yadawa a jihar, cewa wai jami'anta sun kama wasu mutane da ake zargi 'yan Boko Haram ne.

Rundunar ta ce, idan ma akwai wasu mutane da ta kama, ba su da alamun wata nasaba da waccan kungiya.

Karin bayani