Hukumar EFCC tana shirin damke gwamnonin da kotu ta sauke daga mukamansu

Taswirar Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriya

A Najeriya, rahotanni na nuna cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC tana shirin damke wasu tsaffin gwamnonin da kotun kolin kasar ta sauke a ranar Juma'ar da ta gabata.

Bayanai na nuna cewa EFCC din za ta diram ma wadannnan tsaffin gwamnonin ne saboda a yanzu ba su da rigar kariya.

Tsaffin gwamnonin da kotun kolin ta sauke su ne Admiral Murtala Nyako na jahar Adamawa, da Timipre Sylva na Bayelsa, da Liyel Imoke na Cross River, da Ibrahim Idris na Kogi da kuma Aliyu Magatakarda Wamakko na jahar Sokoto.

Da ma dai hukumar ta sami koke-koken cin hanci da wawurar dukiyar jama'a ne a kan gwamnonin, amma ba za ta iya kama su ko tuhumar su ba saboda kariyar da tsarin mulki ya ba su daga kamu idan suna kan mukamin.

A can baya an sami wasu gwamnonin da irin wadannan laifuka, inda aka tilasta wa wasu amayar da irin dukiyar da suka wawura.

Karin bayani