Tawagar hukumar nukiliya ta duniya na ziyara a Iran

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban hukumar IAEA, Yukiya Amano

Masu sa ido daga hukumar makamashi ta duniya IAEA sun isa Iran don fara wata ziyarar kwanaki uku.

Ziyarar za ta mayar da hankali ne a kan shirin nukiliyar Iran da ake ta cece-kuce akansa.

Tawagar, za ta gana da mahukuntan kasar, kuma watakila ma ta ziyarci tashohin nukiliyar kasar don karkare sauran batutuwan da suka rage akan shirin nukiliyar Iran din.

A farkon wannan watan ne Tarayyar Turai da Amurka suka sanyawa kasar takunkumi, suna masu cewa shirin nukiliyar Iran ba na zaman lafiya ba ne, zargin da Iran din ta musanta.

Karin bayani