An hallaka wani dan sanda a Kaduna

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya, wadansu mutane da ba a san ko su wanene ba sun harbe har lahira wani dan sanda a Hayin Rigasa da ke jihar Kaduna.

Maharan dai na kan babur ne inda bayan sun harbe dan sandan suka ranta-a-na-kare.

Rundunar 'yan sandan jihar ta ce 'yan fashi ne suka harbe dan sandan.

Lamarin dai ya firgita mazauna yankin inda suka yi ta gudu don tsira da rayukansu.

Wannan lamari ya faru ne a daidai lokacin da ake fama da tabarbarewar tsaro a kasar.