An yankewa Hamza Al-Mustapha hukuncin kisa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption An dai shafe shekara-da-shekaru ana gudanar da wannan shari'a

A Najeriya wata kotun daukaka kara a jihar Legas ta yanke wa tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha hukucin kisa ta hanyar rataya sakamakon kisan matar marigayi MKO Abiola.

Mai shari'a Mojisola Dada ta ce ya kamata a rataye Majar Hamza Al-Mustapha, sakamakon samunsa da hannu a shirya kisan uwargidan shahararren dan kasuwa kuma dan siyasa marigayi Moshood Abiola.

An dai shafe shekara-da-shekaru ana gudanar da wannan shari'a - wacce ta ja hankalin jama'a a kasar.

Muna dauke da karin bayani.