An yankewa Hamza Al-Mustapha hukuncin kisa

Hamza Al-Mustapha Hakkin mallakar hoto google
Image caption An dai shafe shekara-da-shekaru ana gudanar da wannan shari'a

A Najeriya wata kotun daukaka kara a jihar Legas ta yanke wa tsohon dogarin marigayi Janar Sani Abacha, Hamza Al-Mustapha hukucin kisa ta hanyar ratayewa sakamakon kisan uwargidan marigayi MKO Abiola.

Mai shari'a Mojisola Dada ta ce ya kamata a rataye Manjo Hamza Al-Mustapha, sakamakon samunsa da hannu a shirya kisan uwargidan shahararren dan kasuwa kuma dan siyasa marigayi Moshood Abiola.

Al-Mustapha, shi ne na hannun damar tsohon shugaban mulkin soji Janar Sani Abacha, ya shafe shekaru 13 yana zama a gidan yari, tun bayan da aka zarge shi da shirya kisan.

Wannan shari'a ta ja hankalin jama'a sosai a kasar, musamman ganin lokacin da aka shafe ana gudanar da ita - da ma abubuwan da suka rinka faruwa a lokacin shari'ar.

Zaben 1993

Anta samun shaidu masu cin koro da juna a lokacin shari'ar, yayin da kungiyoyi daban-daban suka nuna damuwa kan yadda aka dade ana gudanar da ita.

A shekarar 1996 ne aka kashe Kudirat Abiola sakamakon wani harbi da wasu mutane suka yi mata.

Marigayi Moshood Abiola ne ake kyautata zaton ya lashe zaben shugabancin kasar da aka gudanar a shekara ta 1993, wanda daga bisani gwamnatin mulkin soji ta Janar Ibrahim Babangida ta soke.

Kuma babu wani abu da yake tunawa 'yan kasar wancan zabe kamar wannan shari'ar.

Sai dai babu tabbas ko wannan hukunci zai kawo karshen sa'insar da shari'ar ta haifar.

Wannan hukuncin ya zo a daidai lokacin da Najeriya ke cikin mawuyacin hali ta fuskar tsaro da kuma siyasa, abinda masu lura da al'amura ke ganin ka iya kara cakuda al'amura a kasar.

Karin bayani