Ana lalubar hanyar bunkasa tattalin arzukin Turai

Taron koli na tarayyar Turai Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Taron koli na tarayyar Turai

Shugabannin tarayyar Turai sun fara wani taron koli a birnin Brussels domin nemo hanyoyin da za su bunkasa tattalin arzikin nahiyar duk kuwa da matakan tsuke bakin aljihun da suke dauka.

Za su maida hankali ne wajen rage adadin marasa aikin yi - wanda ya kai kashi goma cikin dari a kasashen da ke amfani da kudin Euro.

Za kuma a yanke shawara kan tsaurara matakai wurin aiwatar da kasafin kudi, domin samun kudaden tallafi a nan gaba, sai dai babu Burtaniya a wanna tsarin.

Wakilin BBC ya ce wani abu da zai kara cakuda al'amura a taron shi ne shawarar da Jamus ta bayar na Girka ta mika iko da kasafin kudinta ga wani kwamishina na tarayyar - shawarar da Girkan ta yi watsi da ita.

Karin bayani