Sarkozy ya gabatar da sabon haraji a Faransa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Nicholas Sarkozy

Shugaban Faransa, Nicholas Sarkozy, ya fitar da sabbin shirye-shirye da ke da nufin daidaita tattalin arzikin kasar da kuma samar da ayyukan yi.

Shirye-shiryen sun hada da sanya haraji a kan duk wadansu harkokin kudi, wadanda ya ce za su fara aiki daga watan Agusta mai zuwa.

Mista Sarkozy ya gabatar da wadannan shirye-shirye ne a wata hira da ya yi da wani gidan talbijin, watannin uku kafin zaben shugaban kasar.

Ya ce:'' Muna sa ran harajin zai samar da kudaden shiga da suka kai Euro biliyan daya tare da rage gibin kasafin kudin mu. Da zarar an fara amfani da harajin a duk kasashen Tarayyar Turai, to sai tsarin harajin mu ma ya bi sahu''.

Sabon tsarin albashi

Mr Sarkozy ya ce za a yi garambawul ga dokokin kwadago na kasar ta yadda kamfanoni da kungiyoyin kwadago za su daddale game da yanayi aiki da na albashin kananan ma'aikata.

Hakan zai kawo karshen dokar kasar inda ma'aikata kan yi aikin sa'o'i 35 a mako guda.

Ya ce wadannan shirye-shirye za su basu damar sanya kudaden cikin tsarin tallafawa jama'a.

Karin bayani