Dakarun gwamnatin Syria na murkushe 'yan adawa

Mayakan 'yan adawa a Syria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mayakan 'yan adawa a Syria

Rahotanni sun ce, dakarun gwamnatin Syria sun kwace unguwanni da ke kewayen Damascus, babban birnin kasar, inda sojojin da suka fandare suka yi babakere.

Ganin cewa, mahukuntan Syriar sun niki garin murkushe dakarun adawar, a wannan makon hankali zai koma ne zauren Majalisar Dinkin Duniya, inda bisa ga dukan alamu kungiyar kasashen larabawa zata nemi kwamitin sulhu ya tsoma baki.

Sai dai kuma wakilinmu ta fuskar diplomasiyya, Jonathan Marcus na ganin abin da kamar wuya, ganin yadda har yanzu Rasha ke bada cikakken goyon baya ga shugaban Syriar, Bashar al-Assad:

Karin bayani