Ana matsa lamba kan majalisar dinkin duniya game da Syria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sakatare Janar na majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-Moon

Gwamnatocin kasashen yammacin duniya na kara matsin-lamba kan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin ya tsoma baki a rikicin da ke karuwa a Syria.

Kasashen na shirin aikewa da ministocin harkokin wajensu zuwa hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin New York domin su matsawa kwamatin tsaron lamba, don ya amince da kudurin da kungiyar kasashen Larabawa ta gabatar, wanda zai sa shugaba Bashal al-Assad na Syria ya sauka daga kan mulki.

Suna fatan cewa wannan matsin-lamba za ta sauya ra'ayin kasar Rasha wacce ta ki amincewa da duk wani shiri da zai sa a samu sauyin gwamnati a Syria.

Hasalima, ta yi kira ne ga gwamnatin Syria da 'yan adawa da su hau-teburin sasantawa don magance rikicin kasar, kiran da 'yan adawa suka yi watsi da shi.

Sai dai Amurka ta ce tana tattaunawa da Rasha don neman amincewarta ga matakin samun sauyin siyasa a Syria.

A yayin da ake ci gaba da tattaunawa a kan Syria, a can kasar kuwa, rahotanni na cewa dakarun gwamnati na fatattakar 'yan adawa daga wasu unguwannin wajen birnin Damascus, da kuma biranen Homs da Deraa, inda nan ne suke da karfi sosai.

Kazalika rahotannin sun ce akalla mutane arba'in ne dakarun suka kashe a ranar Litinin.

Karin bayani