Rasha ta yi gargadin yakin basasa a Syria idan aka kawar Shugaba Asad

Shugaba Assad Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Assad

Rasha ta yi gargadin cewa kudurin da kasashen Yamma suka gabatar a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ake tattaunawa a kai, zai iya jefa kasar cikin yakin basasa.

An shirya kudurin ne bisa shirin samar da zaman lafiya na kasashen Larabawa, wanda kuma ya nemi Shugaba Bashar Assad ya yi murabus.

Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce kawar da Mr Assad daga mulki zai haifar da karin zubar da jini ne a yankin

Ya ce mutanen da ke da sha'awar kawar da gwamnatoci a yankin Gabas ta Tsakiya, ya kamata su rinka la'akari da abin da ka iya kaiwa-ya-komo.

Masu adawa da shugaba Assad sun yi kira ga Rasha da ta daina goyon bayansa, ko kuma ta rasa damar shiga a dama da ita a al'amuran tattalin arzikin Syriar a nan gaba.

Karin bayani