Farashin kayan abinci ya ragu a duniya

Kayanm abinci
Image caption Akwai yiwuwar kayan abincin su ci gaba da yin sauki

Bankin duniya ya ce a watanni uku na karshen shekarar da ta wuce farashin kayayyakin abinci a duniya ya ragu da kashi takwas cikin dari.

Bankin ya ce farashin alkama ya fadi da kashi 15 cikin dari, ya kara da cewa a wannan shekarar ma akwai yiwuwar kudin abincin zai dada yin kasa.

To amma kuma yayi gargadin cewa, har yanzu kayayakin abincin na da 'yar tsada, kuma farashinsu ya bambanta sosai daga wannan kasa zuwa waccan.

Wakilin BBC ya ce farashin kayayyakin abinci dai na daga cikin abubuwan da aka kyautata zaton sun haifar da tashin-tashinar siyasa a kasashen Larabawa a bara, haka kuma an gudanar da zanga-zanga a shekara ta 2008 lokacin da farshin ya yi tashin gwauron zabi.

Karuwar kayayyaki

Bankin duniya ya ce farashin muhiman kayayyakin abinci ya yi kasa a duniya a cikin 'yan watannin da suka gabata.

Baya ga farashin alkama, haka kuma lamarin yake a batun farashin masara, koda yake dai farashin shinkafa ya dan sauka ne kawai idan aka kwatanta da sauran.

Ya kara da cewa faduwar farashin ya faru ne sakamakon yawaitar kayayyakin abincin da kuma rashin tabbas na tattalin arzikin duniya.

Farashin kayayyakin abinci ya fadi da kashi 14 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Fabarairun bara lokacin da ya yi tsada.

Har ila yau bankin na hasashen cewar za a ci gaba da samun karuwar kayyayakin abinci a kasuwanni abinda kuma zai sakko da farashinsa.

Karin bayani