Amurka ta kai hare-hare a Yemen

Amurka ta kai hare-hare a Yemen Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yemen ta dade tana fama da rikicin siyasa

Rahotanni daga Yemen sun ce, akalla mayaka 13 wadanda ake jin suna da alaka da kungiyar al Qaeda, sun hallaka a wani hari da jiragen saman Amurka suka kai a kudancin kasar.

Jami'ai a yankin sun ce daya daga cikin wadanda aka kashe shi ne jagoran 'yan gwagwarmaya na yankin - Abdel-Munim al-Fathani wanda Amurka ke nema bisa zargin kaiwa jirgin ruwanta hari a shekara ta 2000.

An kuma kai wani harin kan wata tawagar kungiyar ta Al Qaeda da ke tafiya a wata mota.

Wasu majiyoyi a Yemen din sun ce, jiragen saman Amirkan da suka kai hare-haren, jirage ne da basu da matuka.

Ruwa a jallo

An yi luguden wutanne ta sama a lardin kudanci na Abyan, wato yankin da masu tada kayar baya suka samu gagarumin nasara sakamakon tashin-tashinan siyasar dake addabar Yemen.

Kawo yanzu dai Washington bata ce uffan ba amma rahotanni sun nuna cewar an shafe daren jiya ana luguden wuta a wata makaranta da 'yan tada kayar bayan suke tattaunawa wato inda ake tunanin nan ne mattattaran 'yan Al-Qaeda.

Shugabanni a yankin sun bayyana daya daga cikin wadanda suka mutu a matsayin Abdel Munem Al Fatahani, mutumin da dama ake nema ruwa a jallo na lokaci mai tsawo.

Kuma a baya an yita kai masa hari amma kuma ana kuskurewa.

Babu rahotanni akan ko harin ya shafi fararen hula.

Karin bayani