Wani 'mai zanga-zanga' ya mutu a Senegal

Image caption Shugaba Abdoulaye Wade

Akalla mutum guda ne ya rasa ransa a Senegal, lokacin tashin hankali na baya-bayan nan tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zanga a Dakar, babban birnin kasar.

Rahotanni na cewa wata motar 'yan sanda ce ta bi ta kan mutumin, a lokacin zanga-zangar nuna adawa da shawarar shugaba Abdoulaye Wade ta neman wa'adin mulki karo na uku.

'Yan sanda sun harba barkonin tsohuwa domin tarwatsa wani gangami na masu adawa da hukuncin kotun da ya baiwa Mr Wade damar yin tazarce, ya kuma haramta wa wasu mutanen tsayawa takara.

Amurka ta yi gargadin cewa wannan hukunci zai iya illa ga kimar da aka dade ana kallon kasar ta Senegal da ita ta fuskar dimokradiyya da ma zaman lafiyarta.

Haramtacciyar Zanga-zanga

A baya dai Gwamnatin kasar Senegal ta ce zanga-zangar da 'yan adawa suka shirya gudanarwa a kasar haramtacciya ce, sai dai 'yan adawar sun ce ba gudu ba ja da baya.

Kungiyoyin 'yan adawar - da aka fi sani da M23 - suna adawa ne da shirin shugaba Abdullahi Wad na tsayawa takara karo na uku.

Daraktan kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International a Senegal Seydi Gasama, ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar a samu tashin hankali idan 'yan sanda suka yi kokarin hana zanga-zangar.

"Damuwarmu ita ce za a iya jikkata mutane ko ma a kashe wasu, idan 'yan sanda suka yi tawo muga da masu zanga-zangar kamar yadda ta faru a jiya".

Shugaban Cibiyar Raya Demokuradiyya ta Najeriya Dr Jibril Ibrahim wanda ke halartar zanga-zangar a Senegal, ya shaida wa BBC cewa ya je kasar ne domin tabbatar da tsarin demokuradiyya.

Masu zanga-zangar na adawa ne da hukuncin kotun koli wanda ya baiwa shugaba Wad dan shekaru 85 damar tsayawa amma aka hana wasu.

Amurka ta yi gargadin cewa hukuncin zai zubar da kimar da kasar take da ita a fannin demokuradiyya.

An sako wani babban dan adawa

Kungiyoyin kare hakkin dan adam a kasar Senegal sun ce an sako wani jagoran 'yan adawa, Alioune Tine, ba tare da an tuhume shi ba, bayan da 'yan sanda suka tsare shi na tsawon kwanaki biyu.

An kama Mr Tine ne bayan wata tarzoma da ta barke sakamakon wani hukuncin kotu, wanda ya bai wa Shugaba Abdoulaye Wade damar yin tazarce.

A ranar Litinin an kashe mutane biyu sakamakon wani artabu tsakanin 'yan adawa da jami'an tsaro a arewacin kasar.

Kundin tsarin mulkin Senegal ya tanadi wa'adi biyu ga shugaban kasa, sai dai kotun tsarin mulkin kasar ta yanke hukuncin cewa wannan bai shafi wa'adin mulkin shugaba Wade na farko ba, wanda ya fara kafin a amince da sashen na tsarin mulki.

Yayin da kotun ta amince da takarar Mr Wade, a bangare daya ta haramta takarar mawakin nan Youssou N'Dour da kuma wasu 'yan adawa biyu.

Jam'iyyun adawa da kuma masu fafutuka sun yi kiran da a gudanar da zanga-zangar adawa da takarar Mr Wade.

Za a gudanar da zabe ne a ranar 26 ga watan Fabrairu.