Bamabamai sun fashe a Maiduguri

Maiduguri
Image caption Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno dake Arewacin Nigeria na nuna cewa wasu abubuwa sun fashe a daren jiya wadanda ake kyautata zaton cewa bamabamai ne.

Wasu mazauna garin sun ce sun kwana cikin zullumi sakamakon tashin bamabaman.

Tashin bamabaman na zuwa ne bayanda hukumar leken aseri ta farin kaya wato SSS ta ce ta kama wani da ake zargin cewa kakakin kunkiyar Boko Haram ne wato Abu Qaqa.

Kungiyar Boko Haram dai ta yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari biyu a Nijeriyar cikin wata gudan da ya wuce, a sakamakon wasu jerin hare haren bam.

Mun Kama Kakakin Boko Haram

Hukumar leken asiri ta Najeriya SSS, ta ce ta kama mai magana da yawun kungiyar Jama'atu Ahlus-Sunnah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram mai suna Abu Qaqa.

Wata majiya a hukumar ta SSS ta shaida wa BBC cewa an kama mutumin da yake wa kansa lakabi da Abu Qaqa ne ta hanyar amfani da na'urar bin sawun inda mutum yake amfani da wayar salular sa wato GPS.

Hukumar ta leken asiri ba ta kai ga yin cikakken bayanin yadda ta tabbatar da cewa mutumin da ta kama din shi ne Abu Qaqa ba.

Sai dai wata majiya a hukumar ta SSS ta ce hukumar ta shafe watnni tana bin diddiginsa, kuma ya yi ta sauya wurare da lambobin waya.

Hukumar ta SSS ta ce har yanzu tana ci gaba da yi wa mutumin tambayoyi kuma sai nan gaba ne za ta ta yi wa manema labarai karin bayani.

A baya dai hukumar SSS ta taba nuna wa manema labarai wani mutum da ta ce mai magana ne da yawun kungiyar Boko Haram mai suna Usman Alzawahiri, amma daga bisani kungiyar ta Boko Haram ta karyata cewa yana magana da yawunta.

Sai dai wasu bayanai daga kungiyar ta Boko Haram sun tabbatar da cewa an kama Abu Qaqan ne cikin daren jiya, amma wani dan kungiyar wanda bai bayyana sunansa ba, ya shaida wa 'yan jarida a Maiduguri cewa ba za su yi karin bayani ba sai sun samu izini daga shugaban kungiyar Abubakar Shekau.

Bayanai sun ce ba a yi wata musayar wuta ba a lokacin da aka kama shi.

Shi dai Abu Qaqa ya jima yana magana da yawun Boko Haram a matsayin jami'in da ke shiga tsakanin kungiyar da 'yan jaridu.

Karin bayani