Boko Haram: Mutane na ta yin kaura a jihar Sokoto

Barazar Boko Haram Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Boko Haram

Sakamakon barazanar 'yan kungiyar Boko haram na kai hari a Sakkwato, dimbin mutanen da ke zaune a unguwannin dake makwabtaka da babban gidan yarin birnin, da kuma wani babban ofishin 'yan sanda ne suka kauracewa gidajensu, domin fargabar kada hare-haren su rutsa dasu.

Wani mazaunin unguwar ya shaidawa BBC cewar mutane sama da 150 ne, suka yi kaura ya zuwa jiya, kuma wasu na kara ficewa.

A ranar juma'a ne dai kungiyar ta yi barazanar kai hare hare kwatankwancin na birnin Kano in har ba a sako mutanen ta da ta ke zargin an kama a Sakkwaton ba ranar Alhamis.

Sai dai wasu rahotanni sun ce tuni gwamnatin tarayyar kasar ta tura wata runduna ta kwararru kan yaki da ta'addanci domin kare birnin.

Karin bayani

Labaran BBC