An yi zanga-zanga a Masar a kan kashe-kashen da aka yi jiya

'Yan sandan Masar sun harba barkonon tsohuwa don tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Alkahira, wadanda suka fusata da yadda aka samu tashin hankali a filin wasan kwallon kafa na birnin Port Sa'id.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Filin wasa a Masar

Masu zanga-zangar dai sun zargi 'yan sanda da gazawa wajen tabbatar da tsaro a lokacin wasan da aka yi a jiya a birnin.

Mutane 74 ne suka rasa rayikansu bayan da magoya bayan kulob din Al Masri suka yi dauki-ba-dadi da na kulob din Al Ahly da suka kai ziyara a birnin.

Wakilin BBC ya ce a jawabin da ya yi wa majalisar dokoki, Firaministan Masar din ya ce ya dauki alhakin abun da ya faru, amma ya ce matakin da gwamnati ta dauka ya zuwa yanzu, shi ne korar dukannin mambobin Hukumar wasan kwallon kafa ta kasar.

Sai da wakilin namu ya ce jamaa da dama suna zargin cewa magoya bayan tsohon shugaba Mubarak ne suka tada rikicin saboda irin rawar da magoya bayan kulob din na Al Ahly suka taka wajen shirya boren da ya kai ga kifar da gwamnatinsa.

Kwana guda bayan aukuwar tashin hankali mafi muni a tarihin kwallon kafa a Masar, ana cigaba da nuna fushi tare musayar kalamai tsakanin 'yan kasar akan cewar me yasa aka bari lamarin ya auku.

Magoya bayan Al Ahly wadanda sune aka kaiwa hari sun taru a wajen filin wasansu dake birnin Alkahira.Suna ta kewaye birnin a yayinda wasu ke kiran shugaban mulkin sojin kasar field Marshall Tantawi yayi murabus.

Can kuma a majalisar dokoki, Firaministan Masar, Kamal al-Ganzouri ya kori mambobin hukumar dake kula da kwallon kasar

Ya ce, "Matakin farko shine na amincewa da murabus din gwamnan Port Said.

"Na biyu kuma shi ne dakatar da shugaban tsaron Port Said tare da tuhumarsa.mataki na uku shine korar shugaba da mambobin hukumar kwallon Masar daga yau, tare da soma bincike a kansu."

Mutane 74 ne dai suka rasu a Port said lokacin da magoya bayan kungiyar Al Masri suka kaiwa magoya bayan Al Ahly ta Alkahira hari a karshen karawar da suka yi.

A halin yanzu kuma wadanda aka yi tashin hankalin a gabansu, suna bayyana yadda lamarin ya auku, kamar wannan mutumin da bayason a fadi sunansa.

Yace: Muma mun maida martani dan kadan, sai muka ga mutane daya wa.

A don haka sai muka yanke shawarar cewar gwamma mu gudu, amma kuma sai muka ga an rufe kofofin filin wasan.

Muna ta gudu 'yan Al Masri kuma sunata daya bangare.

Sojoji ba su zo ba sai bayan mintuna 20 lokacin da muka riga muka balla kofofin.

Sakamakon lamarin da, an yi kakkausar suka ga gwamnatin mulkin soji a lokacin mahawara a majalisar dokokin Masar.

Kuma an dakatar da gasar kwallon kasar sannan kuma wasu 'yan wasa da masu horaddasu daga kulob din biyu da suka yi taho mu gama sunyi murabus, a yayinda wasunsu ke cewar sun bar kwallon kafa har abada.

Karin bayani