Fiye da mutane 70 sun rasu a rikicin kwallon kafa a Masar

Tashin hanakali a Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tashin hanakali a Masar

A kasar Masar an kira wani taron gaggawa na majalisar ministoci, da kuma na majalisar dokoki, bayan barkewar wani rikici a lokacin wasan kwallon kafa da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla saba'in da hudu, a garin Port Said.

Kafar talabijin ta kasar ta ce majalisar mulkin sojin dake mulki a kasar ta bada umurnin cewa a gudanar da bincike game da lamarin da ya faru.

Jam'iyyar 'Yan uwa Musulmi, wadda ita ce mafi girma a majalisar dokoki ta ce mahukuntan sojan Masar sun ki samar da tsaro, saboda ribar da zasu samu idan aka shiga rudani, don hakan ya kawo cikas ga mika mulki cikin ruwan sanyi.

Tashin hankalin ya fara ne a lokacin wani wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa ta al-Ahli da kuma al-Masri bayan da al-Masri ta samu galaba wanda ba ta saba yi ba.

Majalisar mulkin sojin kasar ta Masar ta ware kwanaki uku don makokin mutane 74 da suka rasu a tashin hankalin.

Karin bayani

Labaran BBC