Rashin aikin yi ya ragu sosai a Amurka

Neman aiki Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Neman aiki

Yawan marasa aikin yi a Amurka ya ragu zuwa kashi 8.3 daga cikin100, abin da ya karfafa fatan da ake da shi na samun farfadowar tattalin arzikin kasar.

Wannan dai shi ne adadi mafi kankanta na yawan marasa aikin yi a Amurka a cikin shekaru ukku da suka wuce.

Alkaluman gwamnati sun nuna cewa an samu karuwar guraben aiki kusan dubu dari biyu da hamsin a watan jiya kadai, fiye da abin da masu sharhi suka yi hasashe.

Shugaba Obama ya nuna farin cikinsa da wannan al'ammari.

Ya ce, "Tattalin arzikinmu yana kara karfi, kuma yana farfadowa cikin sauri.

"Za mu yi duk abin da za mu iya domin wannan cigaba ya dore."

Masu sharhi suna ganin wannan al'ammari zai iya taimaka wa Mista Obama a yunkurinsa na samun wani karin wa'adi mulki.

Karin bayani