An halaka mutane biyu a kasar Masar

Masu zanga zanga a Masar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu zanga zanga a Masar

An kwashe dukkan tsakar daren da ya gabata ana taho mu-gama tsakanin jami'an tsaro da masu zanga-zanga da suka fusata a Alkahira, babban birnin Masar.

Masu zanga-zangar dai na nuna rahin amincewarsu ne da mutuwar masu goyon bayan klub-klub din kwallon kafa su saba'in da hudu ranar Larabar da ta gabata.

Mutane biyu ne suka halaka a birnin Suez sakamakon taho-mu gaman.

Masu zanga zangar dai sun yi imanin cewa da gangan aka kai hari kan magoyabayan kwallon kafa na birnin Alkahira saboda irin rawar da suka taka wurin tunbuke tsohon shugaban kasar Mubarak.

Karin bayani

Labaran BBC