Sakataren makamashin Birtaniya yayi murabus

Chris Huhne Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Chris Huhne

Sakataren Birtaniya mai kula da makamashi, Chris Huhne, ya yi murabus daga kan mukaminsa, bayan da aka tuhume shi bisa zargin cewa ya bukaci tsohuwar matarsa ta dauki wani laifi a madadinsa.

Laifin ya nuna cewa, ya zarta adadin gudu da mota da doka ta kayyade, abun da zai sa a haramta ma shi tuki na wani lokaci.

Mr Huhne da tsohuwar mai dakinsa, Vicky Pryce, suna fuskantar tuhuma ne bisa zargin hana shari'a yin aikinta.

Sai dai dukansu sun musanta aikata ba daidai ba.

Mr Huhne kusa ne a jam'iyyar Liberal Democrats, wadda ta yi kawance da jam'iyyar Conservative don kafa gwamnati.

Karin bayani