Jamaar Kano sun koka da hukumomin tsaro

Jamian tsaron Nigeria Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Jamian tsaron Nigeria

Jama'ar birnin Kano a arewacin Nigeria na kokawa da muzgunawa, a wasu lokutan ma da azabtarwa, gami da karbar kudade da suke zargin jami'an tsaro dake binciken abubuwan hawa na yi musu.

Tun bayan harin bama bamai da aka kai jihar a watan da ya gabata ne dai aka jibge jami'an tsaron domin binciken ababan hawa da kuma tabbatar da tsaro, sai dai jama'a na zargin jami'an tsaron da wuce gona da iri a wasu lokutan.

Sai dai tuni rundunar 'yan sandan jihar tace ta fara daukar matakin ladabtarwa akan duk wani da aka samu da saba ka'idar aikin da doka ta tanada.

A jihar Filato kuwa wasu al'ummomi a karamar hukumar Barikin Ladi na kokawa da yadda dokar hana fita daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe ke ci gaba da aiki a yankin duk da cewa zaman lafiya ya dawo kimanin watanni uku bayan tashin hankalin da yayi sanadiyar kafa dokar.

Karin bayani

Labaran BBC