Yunkurin sasantawa a Sudan ta Kudu ya kai ga kisan mutane 37

Taswirar Sudan ta Kudu

Asalin hoton, a

Bayanan hoto,

Taswirar Sudan ta Kudu

Wani yunkurin sassantawa tsakanin wasu kabilu a Sudan ta Kudu, ya haifar da musayar wuta tsakanin 'yan sanda, abin da ya yi sanadiyyar hallaka mutane talatin da bakwai.

Tashin hankalin ya faru ne a jihar Unity, lokacin da jami'ai ke gaanawa domin tattaunawa a kan wani rikicin kabilanci da ya auku a farkon wannan makon, wanda ya haddasa asarar rayuka da dama.

Wakilin BBC ya ce wani jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya ce wata takaddama ce ta barke, sannan wasu manyan motoci hudu suka isa wurin cike da 'yan sanda, wadanda suka yi ta harbi irin na mai kan mai tsotsayi.

Daga cikin mamatan har da fararen hula.

Kungiyoyin kare Hakkin Bil-adama sun soki lamirin jami'an tsaro bisa rashin ladabin da suka nuna.