An tsaurara matakan tsaro a Adamawa yayinda ake shirin zabe

Zaben Adamawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zaben Adamawa

Ana shirye shiryen fara zaben gwamna a jihar Adamawa dake arewacin Nigeria.

Tuni aka tsaurara matakan tsaro a jihar don kaucewa yiwuwar fuskantar duk wani kalubalen tsaro da ka iya tasowa.

Fafatawa tafi zafi ne tsakanin Vice Admiral Murtala Nyako mai ritaya, na jam'iyyar PDP, da kuma tsohon gwaamnan mulkin soja a jihar Lagos, Brigadier Janar, Buba Marwa mai ritaya na jam'iyyar CPC.

Zaben dai shine na farko da hukumar zaben kasar INEC za ta gudanar bayan da kotun kolin kasar ta yanke hukunci kan waadin wasu gwamnoni biyar a kasar, wanda ta ce tuni suka kare watanni da suka gabata.