Ana ci gaba da zaben gwamna a jahar Adamawa

Ana zaben gwamma a jahar Adamawa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana zaben gwamma a jahar Adamawa

A Najeriya yanzu haka jama'a a jahar Adamawa na ci gaba da kada kuri'ar zaben gwamnan jahar, karkashin tsauraran matakan tsaro.

Tuni dai aka tsaurara matakan tsaro inda aka girke dubban jami'an tsaro ciki har da wadanda aka tura jihar daga wasu jihohin kasar, domin kula da sha'anin tsaro a lokacin zaben.

Ana ganin fafawa tafi zafi tsakanin Vice Admiral Murtala Nyako mai ritaya, na jam'iyyar PDP, da kuma tsohon gwamnan mulkin soja a jihar Lagos, Birgediya Janar, Buba Marwa mai ritaya, na jam'iyyar CPC.

Karin bayani