An kashe fiye da mutane dari biyu a birnin Homs

An kai farmaki a Homs
Image caption An kai farmaki a Homs

Masu fafutuka a Syria sun ce, fiye da mutane dari biyu sun hallaka, a wani farmakin da sojojin gwamnati suka kai a birnin Homs.

Gwamnatin Syria dai ta musanta cewa dakarunta sun yi barin wuta a Homs din.

Ta kuma dora alhakin kashe kashen akan wadanda ta kira, kungiyoyin 'yan ta'adda masu dauke da makamai.

Can kuma a majalisar dinkin duniya, ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya ce, abin kunya ne idan har a yau, majalisar ta kada kuri'ar amincewa da wani daftarin kuduri, mai yin Allah wadai da tashe tashen hankulan da ke faruwa a Syriar.

Karin bayani