Obama ya sa hannu akan dokar matsawa Iran kaimi

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban Amurka Barrack Obama ya sanya hannu akan wata doka da ke tsaurara takunkumi akan kadarorin Iran dake karkashin ikon Amurkar.

Ma'aikatar kudin Amurka ta ce sabbin takunkumin za su shafi kadarorin ma'aikatun gwamnatin Iran. Takaunkumin zai kuma shafi kamfanoni mallakar gwamantin Iran dake Amurka, har da ma na babban bankin Iran dake lura da kudaden da kasar ke samu ta hanyar man fetur.

Kasar Amurka ce ke kan gaba wajen tilastawa Iran ta daina shirin ta na nukiliya.