Za'a gurfanad da masu fafutuka a Masar

Masu fafutuka a Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu fafutuka a Masar

A Masar, wasu mutane fiye da arba'in, ma'aikatan kungiyoyin kare hakkin bil'adama da kuma masu fafutukar girka demokradiyya, zasu gurfana a gaban kotu.

Ana zarginsu ne da gudanar da aikace-aikacensu ba bisa ka'ida ba, da kuma samun kudade daga kasashen waje, wadanda suke amfani da su wajen tada zaune tsaye a Masar din.

Dayawa daga cikin mutanen 'yan kasashen waje ne da suka hada da Amirkawa 19 da kuma 'yan kasar Jamus.

Wakiliyar BBC ta ce, sojojin da ke mulki tun shekara daya da ta wuce, sun sha zargin 'yan kasashen waje da hannu a zanga zangar da ake a kasar, da kuma kokarin yamutsa kasar.

Karin bayani