Mitt Romney yayi nasara a jihar Nevada

Mitt Romney yayi nasara a Nevada Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mitt Romney yayi nasara a Nevada

A cigaba da zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican a Amurka, sakamakon farko daga jihar Nevada na nuna cewa, Mitt Romney ne yayi nasara.

Mista Romney dai ya lashe kusan kashi araba'in na dukkan kuri'un da aka kada ya zuwa yanzu a zabukan fidda gwanin jam'iyyar ta Rupublican.

Wannan dai yasa ya shiga gaban abokan karawarsa da suka hada da Newt Gingrich da kuma Ron Paul:

Karin bayani

Labaran BBC