MEND ta fasa bututun mai na Agip

Masu fafutukar yankin Niger Delta Hakkin mallakar hoto b
Image caption Masu fafutukar yankin Niger Delta

A Najeriya, kungiyar MEND mai fafutuka a yankin Niger Delta ta ce, ita ce ta kai hari akan wani bututun mai, mallakar kamfanin AGIP na Italiya.

Shaidu sun ce, a daren jiya sun ga wuta na tashi daga bututun man Nembe-Brass, a jahar Bayelsa.

Kamfanin man na AGIP dai bai ce komi ba game da lamarin.

Kungiyar MEND ta kwashe shekaru tana yiwa masana'antun mai zagon kasa a yankin na Niger Delta.

To amma ta yi sanyi tun bayan da ta karbi ahuwar da gwamnatin tarayya ta yiwa masu fafutuka, a shekara ta 2009.

Karin bayani