Dakarun Syria na luguden wuta a Homs

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun sojin Syria

Rahotanni daga Syria na cewa dakarun sojin kasar na matsa kaimi wajen yin luguden- wuta a kan birnin Homs a ranar Litinin.

Da alamu dakarun Syrian na amfani ne da manyan makamai, suna kuma harba su daga nesa.

A birnin Homs, da dama daga cikin mutanen da suka samu raunuka na karbar magani a asibitocin jeka na- yi- ka.

Rahotannin sun ce an binne matattu cikin daren ranar Lahadi saboda farbaga.

'yan adawa sun fusata

'Yan adawar kasar dai na cike da fushi game da matsayin da kasashen Rasha da China suka dauka na hawa kujerar na-ki akan wani kudurin Majalisar Dinkin Duniya da ya soki gwamnatin Syrian.

Wasu mazauna birnin Homs na fargabar cewa hawa kujerar nakin zai kara karfafawa gwamnatin Syria gwiwa don yin abin da ta ga dama.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton, ta ce dole masu sha'awar ganin an kafa dimokradiyya a Syria su hadewa shugaba Assad kai.

A cewar Hillary Clinton din, kasashen Rasha da China sun karya lagon kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya, lokacin da suka hau kujerar na-ki a ranar Asabar.

Ta ce, babu adalci a matakin, kuma ta bukaci a kawo goyon baya ga 'yan adawar Syriar.

A ganin masu aiko da rahotanni, watakila a yanzu kasashe masu adawa da gwamnatin Assad, za su ci gaba da kokarin kawo karshen zub da jini a Syriar - amma ba ta hanyar majalisar dinkin duniya ba.

Mai yiwuwa su kafa wata kungiya, irin kungiyar tuntubar juna a kan Libiya, wadda ta yi ruwa ta yi tsaki wajen kawar da Kanar Gaddafi.

Karin bayani