Gwamnatin Ghana ta janye karin farashin mai

Shugaba John Atta Mills Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba John Atta Mills

Gwamnatin Ghana ta ba da sanarwar janye karin farashin man petur.

Hakan ya zo yayin da hadaddiyar kungiyar kwadagon kasar, wato TUC, ke shirin fara wani yajin aikin gama-gari, don nuna adawa da karin da gwamnatin ta yi.

Watanni biyu kenan da gwamnatin ta yi karin kashi 20 cikin 100 ga farashin man fetur din.

Gwamnatin Ghanar dai ta janye sabon farashin ne, bayan wata ganawa da mataimakin shugaban kasar, Mr John Mahama ya yi da shugabannin kungiyar kwadagon kasar, a karshen makon jiya.

Karin bayani