Dakarun Syria na yin luguden wuta a Homs

Luguden wuta a Homs Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Luguden wuta a Homs

Sojojin gwamnatin Syria sun yi ta harba harsasai da rokoki babu kakkautawa a birnin Homs.

Wani wakilin BBC a birnin ya ce, tun daga karfe shida na safiyar ranar Litinin ne, shi da kansa ya ga ana ta luguden wuta da manyan bindigogi a unguwannin da jama'a ke zaune.

Mazauna birnin sun shaida masa cewa, wannan ne hari mafi muni da dakarun gwamnatin Syriar suka kai, tun bayan soma boren, kusan shekara daya kenan.

Kuma a duk lokacin da suka yi harbin, ana jin karar abin da suka harbe a kan tituna da unguwanni daban-daban na birnin.

Wani Video da 'yan adawa suka sanya a intanet, ya nuna yadda aka kai hari kan wani waje da suka ce asibiti ne a gundumar Baba Amr, duk da yake ba a tabbatar da ingancin videon ba.

Videaon ya nuna mutanen da aka kashe da kuma wadanda suka samu raunuka, wasu sanye da kayayyakin aiki na asibiti, yayin da mutane ke ta ihu suna neman agaji

Jakadan Rasha zai je Damascus

Yayin da ake ci gaba da kai hare-hare a Syriar dai, a ranar Talata ne ake sa ran Ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, zai isa babban birnin kasar Syria Damascus domin tattaunawa tare da Shugaba Bashar Al Assad.

Tattaunawar da za su yi na zuwa ne bayan da kasashen yamma ke cike da fushin cewar Rashan ta hana Majalisar Dinkin Duniya daukar mataki akan Shugaban Syria.

Amurka ta rufe ofishin jakadancinta a birnin Damascus.

Ma'aikatar harkokin wajen Amirkan ta ce, jakadan kasar a Syria, Robert Ford, ya bar kasar tare da sauran ma'aikatan ofishin jakadancin da su ka rage.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Amirkan, hukumomin Syriar sun kasa daukar matakan da suka dace, na tabbatar da tsaron jami'an diplomasiyyar ta.

Karin bayani