Mandela yana santi idan yaci masara da wake

mandela Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nelson Mandela mai shekaru casa'in da biyu

Matar dake girkawa Nelson Mandela abinci ta kaddamar da wani littafi akan girke- girke inda ta bayyana ire-iren abinci da tsohon shugaban kasar yafi so.

Littafin na Xoliswa Ndoyiya ya yi bayani akan wasu ire iren abinci guda sittin da biyu na gargajiya wadanda Mista Mandela ke santinsu.

Matar ta shafe fiye da shekaru ashirin ta na girkawa iyalan Mandela abinci.

Littafin wanda yana daga cikin litattafan koyon girki a Afrika ta Kudu na kunshe da wasu abincin gargajiya, kuma nan da wasu 'yan watanni za a kai littafin Birtaniya.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da littafin, jikan Mista Mandela wato Luvuyo Mandela ya bayyana Ms Ndoyiya a matsayin wacce ta mutunta sirrin iyalan gidan Mandela.

A cewarsa "UMam'Xoli ta wuce mai girka abinci, ta zama uwa".

Litaffin mai suna Ukutya Kwasekhaya ya bada bayanai akan irin dandanon abincin gidan Nelson Mandela tare da yadda ake girka farfesun kaji, da umqusho wato (masara da wake), da kuma umsila wenkomo wato (miyar jelar saniya).

Image caption Xoliswa Ndoyiya mai girkawa Mandela abinci

Ms Ndoyiya mai shekaru 49 ta dauki abinci a matsayin hanyar kara dankon zumunci a tsakanin iyali da kuma hanyar kawo tunani mai dorewa.

A cikin littafin Ndoyiya ta rubuta cewar "Nelson Mandela ya gaya mini cewar duk ranar da na yi masa koko, yana tunawa da yadda mahaifiyarsa ke masa girki".

An dai kashe mijinta a tashin hankalin da ya faru a shekarar 1990 a tsakanin jami'ar ANC ta su Mandela da kuma Inkatha Freedom Party.

Jim kadan bayan mutuwar mijinta sai aka gabatar da ita gaban Mista Mandela wanda a lokacin yake bukatar mai girka masa abinci.

Ta fara masa aiki a shekarar 1992, shekaru biyu kafin ya zama zababben shugaban kasar Afrika ta Kudu na farko.

Mandela mai shekaru 93 da haihuwa yayi ritaya daga aiki ne a shekara ta 2004.

A halin yanzu dai yana hutawa ne a gidansa dake kauyensu na Qunu dake gabashin Cape da kuma Johannesburg.