An nada Ribadu shugaban kwamitin sa'ido kan kudaden mai

Nuhu Ribadu
Image caption Nuhu Ribadu ne ya yiwa jam'iyyar ACN takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nada Malam Nuhu Ribadu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa ta ACN a zaben da ya gabata, a matsayin shugaban wani kwamiti na musamman da zai sa ido sosai akan kudin shiga daga fannin man fetur.

Wakilin BBC a Abuja Isa Sanusi ya ce kwamitin mai mambobi ashirin bisa ga dukkan alamu wani martani ne ga korafin wasu 'yan Najeriya dangane da abinda suka kira, rufa-rufa a harkar ciniki da kuma kudin shigar fannin man fetur na kasar.

Wata sanarwa da ke dauke da sa hannun babban sakataren ma'aikatar man fetur ta Najeriya, Goni Sheik ce ta bayyana nadin Malam Nuhu Ribadun a matsayin shugaban kwamitin dake da mambobi sha tara.

Sanarwar wacce aka fitar a ranar Talata ta ce, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa wannan kwamiti ne da nufin biyan abinda ya kira bukatar 'yan Najeriya ta ganin cewa, ana baje komai a faifai dangane da harkar man fetur a Najeriya.

Sanarwar ta kuma ce, an dorawa kwamitin alhakin yin aiki tare da kwararru domin tantance hakikanin kudin shiga daga fannin man fetur da ke shiga aljihun gwamnatin Najeriya.

Kwamitin zai kuma sa ido da kuma tantance yawan man da Najeriya ke kaiwa kasuwa da ma yadda gwamnati ke sayar da danyen man a kasuwar duniya, da kuma tabbatar da cewar, ana biyan gwamnati hakikanin kudin da ya kamata daga cinikin man fetur din.

Nuhu Ribadu shi ne ya yiwa jam'iyyar adawa ta ACN takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata.

Sai dai wakilinmu ya ce babu tabbas ko Nuhu Ribadu zai nemi izinin jam'iyyarsa ta ACN kafin ya karbi mukamin, ko kuma zai yi gaban kansa.

Bisa ga dukkan alamu dai kafa wannan kawamiti da Malam Nuhu Ribadu zai shugabanta, ba zai rasa nasaba da zargin yin rufa-rufa, da kuma rashin tabbas da wasu 'yan Najeriya ke yi dangane da kudin shiga da Najeriya ke samu daga harkar man fetur.

Sai dai kuma abinda yanzu mutane za su fi maida hankali akai shi ne ko wannan kwamiti zai yi wani tasiri wajen kawo karshen sama da fadi da ake zargin ya yi katutu tsawon shekaru da dama a fannin man fetur a Najeriya?

Karin bayani